Kashi 1 bisa 3 na ’yan Najeriya duk jahilai ne - Ministan Ilimi

Kashi 1 bisa 3 na ’yan Najeriya duk jahilai ne - Ministan Ilimi

Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa yawan jahilai da ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya sun kai kusan miliyan 60, wato kenan a takaice kashi 1 bisa 3 na daukacin mutanen Najeriya duk jahilai ne.

Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa yawan jahilai da ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya sun kai kusan miliyan 60.

Adamu ya fadi haka ne a jihar Kano, a ranar Laraba, 5 ga wata Disamba inda ya ce wadannan jahilai da ya ke magana a kai, duk matasa ne da kuma magidanta.

Kashi 1 bisa 3 na ’yan Najeriya duk jahilai ne - Ministan Ilimi
Kashi 1 bisa 3 na ’yan Najeriya duk jahilai ne - Ministan Ilimi
Asali: UGC

Ya ce tunda an kiyasta cewa adadin ‘yan Najeriya sun kai miliyan 180, hakan kenan ya na nufin kashi 1 bisa 3 na daukacin mutanen Najeriya duk jahilai ne kenan.

Ministan wanda ya samu wakilcin Mataimakin Darakta na Fannin Ilimin Firamare da Sakandare, Prince James, ya yi bayanin ne a taron shekara ta 2018 na murnar zagayowar Ranar Ilimi ta Duniya.

Ya kara da cewa kashi 60 bisa 100 na marasa ilimin duk mata ne, yayin da Najeriya ke da yara kanana har miliyan 11 wadanda ke yawo a gari, ba su zuwa makaranta.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yi umurnin kama jigon APC a Rivers kan zargin yunkurin aikata kisan kai

Ya ce akwai bukatar a yi gaggawan shawo kan wannan babbar matsala, ganin cewa Najeriya na hankoron cimma kudirin ta na kawar da jahilcin karatu da rubutu da rashin ilimin gaba daya nan da shekara ta 2030.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel