Yanzu-yanzu: An fara zaman majalisar zantarwa na musamman a Aso Villa

Yanzu-yanzu: An fara zaman majalisar zantarwa na musamman a Aso Villa

Wata zaman majalisan zantarwan tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta kankama a fadar shugaban kasa, Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja a ranan Juma'a, 7 ga watan Disamba, 2018.

Ana wannan zama ne domin tattaunawan karshe kan kasafin kudin 2019 kafin gabatar da shi gaban majalisar dokokin tarayya.

Gwamnatin tarayya tana son gabatar da kasafin kudin N8.6 Trillion sabanin N9.12tn da ta yi na shekarar 2018.

Mun kawo muku a wannan mako shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai jagoranci wani muhimmin zaman majalisa na musamman domin aiwatar da shirye-shirye na gabatar da kasafin kudin 2019 kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zantarwa da ya gudana a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a yau Laraba, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shine ya jagoranci zaman majalisar da ya gudana cikin fadar shugaban kasa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Mista Adesina ya bayyana cewa, zaman majalisar na musamman da za ya gudana a ranar Juma'a karkashin jagorancin shugaba Buhari, za ya tattauna kan al'amurran da suka shafi sabon kasafin kudin 2019 domin gabatar da shi zuwa ga Majalisar dokoki ta tarayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel