El-Rufai ya shiga dimuwa – Tambuwal ya yi ba’a ga gwamnan Kaduna

El-Rufai ya shiga dimuwa – Tambuwal ya yi ba’a ga gwamnan Kaduna

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba ya caccaki takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan furucin da yayi game da kamfen din jam’iyyar PDP da ya gudana a yankin arewa maso yamma a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba.

Tambuwal ya bayyana cewa takwaran nasa yayi furucin ne sakamakon durkushewar farin jinin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a tsakanin yan Najeriya a yan kwanakin nan.

El-Rufai ya shiga dimuwa – Tambuwal ya yi ba’a ga gwamnan Kaduna
El-Rufai ya shiga dimuwa – Tambuwal ya yi ba’a ga gwamnan Kaduna
Asali: Twitter

A cewar wani jawabi ga manema labarai, Tambuwa ya tabbatar da cewar gazawar jam’iyya mai mulki ne ya haddasa wa PDP samun shahara yayinda suke firgita jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole

A wani jawabi a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba daga Akibu Dalhatu, hadimin Gwamna Tambuwal wannan martani ne kai tsaye ga Gwamna El-Rufai da yayi ikirarin cewa dandazon jama’a da suka halarci kamfen din PDP a ranar Litinin ba ya Najeriya bane, cewa anyo hayarsu ne daga kasar Nijar.

A wani lamari na daban, mun ji cewa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba ya tattara kayan sa ya bar Jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda mu ka samu labari.

Na’abba ya soki tsarin Jam’iyyar da ke mulkin Najeriya. Kamar yadda labari ya iso mana, tsohon Shugaban Majalisar Kasar ya aikawa Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin sa da ke cikin Unguwar Sharada a cikin Birnin Garin Kano takarda inda ya bayyana ficewar sa daga Jam’iyyar.

Ghali Na’Abba ya tsere daga APC ne a tsakiyar makon nan inda ya bayyana yadda Jam’iyyar ta ke juya Kasar a matsayin dalilin sa na canza-sheka. Na’Abba yace kowa ya san irin halin da Jam’iyyar ta jefa al’ummar Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel