2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole

2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole

Kwamrad Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa sabbin yan takarar gwamna a APC 20 da gwamnoni masu ci guda tara ne za su yi takarar kujerar gwamna a zaben 2019.

Ya bayyana hakan ne lokacin wani taron tattaunawa da kwamitin jam’iyyar ta yi da yan takarar kujerar gwamna a zaben 2019, shugabannin jihad a kuma sakatarorin jam’iyyar na jihad a kasa a Abuja a ranar Ahamis, 6 ga watan Disamba.

2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole

2019: Gwamnonin 9 masu mulki, da sabbin yan takara 20 ne za su yi takarar gwamna a APC - Oshiomhole
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Oshiomhoe ya shawarci yan takarar gwamna akan sukar nasarorin gwamnoni masu barin gado sannan ya shawarce su da kada su yi abunda ya saba ka’ida a lokacin kamfen.

Ya ci gaba da sukar wadanda suke yi ikirarin cewa babu zaben fidda gwani, inda ya bayyana su a matsayin masu adawa da basa neman mafita.

KU KARANTA KUMA: APC ba ta da alkibla don haka na fice na bar ta – Inji Ghali Na’Abba

Ya bukaci shugabannin jam’iyyar a jiha da su yi aiki kai-da-kai da dukkanin yan takarar ta hanyar tabbatar da cewar sun yi nasara a dukkan matakai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel