Kotu ta tura mutane 8 gidan yari bisa laifin fille kan dan sanda

Kotu ta tura mutane 8 gidan yari bisa laifin fille kan dan sanda

A jiya, Laraba, ne wata babbar kotu dake jihar Filato ta bayar da umarnin tsare wasu mutane 8, da ake tuhuma da datse kan wani jami'in dan sanda, a gidan yari.

Ana zargin mutanen 8; Abubakar Sani, Abubakar Mohammed, Hussaini Musa, Mohammed Zubairu, Abdullahi Moammed Doma da Sadiq Abubakar, da aikata laifin kisan kai.

Dan sanda mai gabatar da kara, E. A. Inigbenoise, ya shaidawa kotun cewar wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Satumba.

Ibigbenoise ya ce wadanda ake zargin sun kaiwa dan sanda, Saja Yunana Ishaya, farmaki da gatari tare da datse masa kai a daidai Otal din Girdons dake kan titin zuwa Zaria a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Kotu ta tura mutane 8 gidan yari bisa laifin fille kan dan sanda

Jami'an 'yan sanda
Source: Depositphotos

Ya kara da cewar wadanda ake sun aikata laifin ne bisa dogaro da wani asiri da zai sa su bace, a kasa ganinsu bayan sun aikata laifin.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Yobe tayi feshin maganin gafiyoyi a makabartu

Kazalika ya bayyana cewar laifin ya saba da sashe na 97, 221, da 217 na kundin fenal kod.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin aikata kisan dan sandan.

Jastis A. I Ashoms, alkalin kotun, ya bayar da umarnin tsare mutanen 8 a gidan yari tare da daga karar zuwa ranar 14 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel