Yanzu Yanzu: Ministan muhalli ya zama sarkin Nasarawa

Yanzu Yanzu: Ministan muhalli ya zama sarkin Nasarawa

Karamin ministan muhalli, Usman Jibrin ya zama sarkin garin Nasarawa na 13, a karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Nasarawa.

Mista Jibrin wanda ya kasance shugaban ma’aikatar tun bayan barin tsohuwar minister, Amina Mohammed ya zamo sarkin a zaben da aka yi.

Kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran sarata na jihar, Iliya Osegbe ne ya sanar da hakan a gidan gwamnati da ke Lafia a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba.

Yanzu Yanzu: Ministan muhalli ya zama sarkin Nasarawa

Yanzu Yanzu: Ministan muhalli ya zama sarkin Nasarawa
Source: Facebook

Ya ce Gwamna Tanko Almakura ya amince da zabar Mista Jibril a matsayin sabo sarki. Gwamnan ya kuma amince da zabar Lawrence Ayih a matsayin sabon Abaga Toni na masarautar Toni da ke jihar Nasarawa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Bayan kayar da Buhari da zan yi harda ritaya zan yi masa – Atiku

Ana sanya ran Mista Jibrin zai mika takardar ajiye aiki a matsayin minister kafin ya hau sabon matsayinsa a matsayin sarki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel