Kasar Najeriya ta sake daukar na 3 a Duniya a jerin ta’addanci

Kasar Najeriya ta sake daukar na 3 a Duniya a jerin ta’addanci

Mun samu labari daga Jaridar nan ta Premium Times cewa an fitar da jerin Kasashen da su ka fi kowane fama da masifar ta’addanci a Duniya, a wannan shekarar ma dai Najeriya ta zo cikin sahun farko.

Kasar Najeriya ta sake daukar na 3 a Duniya a jerin ta’addanci

Najeriya da Iraq su na sahun gaba a jerin Kasashen da ke fama da ‘Yan ta’adda
Source: Facebook

A wannan shekara ma, Najeriya ta zo ta 3 a kaf Duniya a cikin jeringiyar Kasashen da ke fuskantar hare-haren ‘Yan ta’adda. A 2014 dai Najeriya tazo 4 a Duniya, sai dai tun bayan nan ne kasar ta makale a matsayin ta 4 a Duniya.

Yanzu haka dai Kasar Iraki ce ta farko a wannan jerin da aka fitar, sannan kuma Kasar Afghanistan. Bayan Najeriya kuma akwai Kasar Syria wanda ta zo na 4 a bana. Kasar Pakistan ce dai ta zo ta 5 a halin yanzu kamar yadda mu ka ji.

KU KARANTA: Mota ta kashe wasu Magoya bayan PDP a kan titi bayan taron siyasa

Ana fama da rikicin ‘Yan ta’addan Boko Haram da kuma rigimar Makiyaya a halin yanzu a Najeriya Rigimar Makiyaya dai yayi sanadiyyar dinbin mutanen da su ka haura adadin wadanda ‘Yan Boko Haram su ka kashe a shekarar nan.

Sauran kasashen da su ke wannan sahu sun hada da: Somaliya, Indiya, Yemen, Masar da kuma Kasar Philippines wanda ta zo ta 10. Binciken da aka yi dai ya nuna cewa abubuwa su na lafawa a Najeriya a cikin shekarun baya-bayan nan.

A baya kun ji cewa ‘Dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai yi wa tsarin kasar nan garambawul, wanda da zarar an yi hakan, Boko Haram za ta rasa tubulin dafawa a Arewacin Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel