Wasu manyan ‘Yan PDP sun mutu a mummunan hadarin mota a Sokoto

Wasu manyan ‘Yan PDP sun mutu a mummunan hadarin mota a Sokoto

Daily Trust ta rahoto labari cewa akalla mutum 5 ne su ka rasu a wani hadarin mota da aka yi a kan hanyar Sokoto zuwa wani Gari. Wadannan Bayin Allah sun kasance manyan ‘Yan Jam’iyyar adawa ta PDP.

Wasu manyan ‘Yan PDP sun mutu a mummunan hadarin mota a Sokoto

'Yan PDP sun yi hadari bayan taron yakin neman zaben Atiku
Source: Depositphotos

Wannan mummunan abu ya faru ne a kan titin Sokoto zuwa cikin Garin Isa inda mutane 5 su ka sheka barzahu a nan take. Kamar yadda labari ya zo mana, wasu mutane 14 sun yi raga-raga sakamakon aukawa gingimari da su kayi.

Haka kuma an samu mutane 49 da su ka samu kananan rauni a hadarin. Wadannan Bayin Allah dai sun doshi wani mai katuwar mota ne bayan sun taso daga wajen taron yakin neman zaben Atiku Abubakar da aka yi a cikin Garin Sokoto.

KU KARANTA: Atiku yace zai yi irin abin da Jonathan yayi wajen inganta tattalin Najeriya

Majiyar ta kuma bayyana cewa an kara samun wasu mutane da su ka mutu a kan hanyar kashegari a dalilin lalacewa babban titin. Tuni dai Mataimakin Gwamnan Jihar, Maniru Dan Iya ya aika da ta’aziyya ga Iyalin da wannan musifa ta shafa.

Hadimin Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto watau Aminu Abdullahi ya aikawa al’ummar Jihar da sakon jaje. Daga baya kuma dai Mataimakin Gwamnan da Shugaban PDP na Jihar Sokoto sun ziyari wadanda su ke kwance a gadon asibiti.

Rabiu Kwankwaso yayi magana wajen bude yakin neman zaben PDP da aka yi a Sokoto inda yace Atiku Abubakar ne ‘Dan takarar da zai samawa Matasa aikin yi. Tsohon Gwamna Kwankwaso yayi kira ga mutane su fito su zabi Atiku a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel