An kulle mahaifina a kurkuku saboda ya yi kokarin hana ni zuwa makaranta - Atiku

An kulle mahaifina a kurkuku saboda ya yi kokarin hana ni zuwa makaranta - Atiku

Tsohon shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya sha wahala da gwagwarmayar rayuwa, musamman yadda ya sha wahala yayin da yake karami.

A watan Janairu na shekarar 1954 ne Ali Kawa, yayan mahaifiyar Atiku da ya yi karatun yaki da jahilci, ya saka Atiku a makarantar firamare ta garin Jada ba tare da sanin mahaifinsa ba.

Atiku, a ciki wani littafi na takaitaccen tarihin rayuwar sa da ya rubuta, ya bayyana yadda ya ji haushin an saka shi an makarantar boko tare da kokarin cire shi daga makarantar.

Atiku ya fadi dalilin da yasa aka kulle mahaifinsa a gidan yari

Atiku ya fadi dalilin da yasa aka kulle mahaifinsa a gidan yari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Albashi ne zai nuna alkiblar ma'aikata a zaben 2019 - Kungiyar Kwadago

Hakan ya jawo aka gurfanar da mahaifin nasa a gaban Alkali tare da yi yanke masa biyan tara. Sai dai mahaifin nasa ya ki biyan tarar kasancewar bashi da kudi. Hakan ne ya sa aka tura shi zuwa gidan yari har sai da kakar Atiku ta wajen uwa dake sana'ar sayar da sabulu ta tara kudi ta biya tarar da aka saka wa mahaifinsa sannan aka fitar da shi daga gidan yarin.

"Ba a son ran mahaifina na yi karatu ba. Yunkurin ya cire ni daga makaranta ne ya jawo aka gurfanar da shi a gaban Alkali aka yi masa tara. Rashin kudin da zai biya tarar ne ya sa Alkali ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari, inda ya shafe wasu kwanaki kafin kakata ta hada kudi ta biya tarar," a kalaman Atiku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel