Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja (hotuna)

Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja (hotuna)

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama wasu yan damfara ta intanet su tara wadanda aka fi sani day an Yahoo-Yahoo a Abuja.

An kama masu laifin ne a ranar 30 ga watan Nuwamba ta hanyar rahoton kwararru da hukumar ta samu akan ayyukan damfara da wajen zaman yan damfarana hanyar fili jirgin sama na Abuja, inda suke guanar da rayuwar da tafi karfin su.

Jami’an EFCC sun gudanar da aiki sanya idanu na tsawon kwanaki akan ayyukan yan damfaran kafin su far masu.wadandaaka kama sune; Edwin Ogbomwan, Okouromi Franklin, Oseji Collins, Collins Onyekwuluje, Anyanechi Ekene, Tony Oviasuyi, Chidi Emeshili, Osaigbovo Aiseos da kuma Osaigbovo Ikponmnosa.

Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja (hotuna)
Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja
Asali: Facebook

Masu laifin sun mayar da gidansu wajen tara yan damfara inda suka mayar da wajen ofishinsu tare da kwanfuta, wayoyi, layukan waya a auran abubuwan damfarar ya Najeriya dama yan kasar waje kudadensu da muhimman abubuwa.

Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja (hotuna)
Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja
Asali: Facebook

Sun yi katunan shaida da sunaye irin su Thomas Jerry Star da John Ben.

KU KARANTA KUMA: Rayuwar auren jarumin kwallon kafa Ahmed Musa

Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja (hotuna)
Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja
Asali: Facebook

Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja (hotuna)
Hukumar EFCC ta kama manyan yan damfara ta intanet 9 a Abuja
Asali: Facebook

Shekarunsu na tsakanin 19 zuwa 26 inda aka kama su da mota kirar GLK Mercedes Benz guda biyu, Toyota Camry guda, Lexus Jeep da wasu kadarori na miliyoyin naira, wanda suka mallaka daga ayyukan damfara.

A Yanzu suna ba hukumar hadin kai sannan za’a mika su kotu da zaran an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel