Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Benue, ta lalata muhimman abubuwa

Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Benue, ta lalata muhimman abubuwa

An samu tashin hankali a gidan gwamnatin jihar Benue, a Makurdi a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba lokacin da wani bangare na ginin ya kama da wuta.

Jaridar Sun ta ruwait cewa koda dai ba’a rasa rai ba a cewar idanun shaida, lamarin ya gurguntar da lamura a bangaren inda ma’aikata suka fit suka ajiye ayyukansu.

Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Benue, ta lalata muhimman abubuwa

Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Benue, ta lalata muhimman abubuwa
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa wata majiya cikin gidan gwamnatin tace gobarar ta fara ne da misalin karfe 1:00 na rana daga transpoman da ke kusa dad akin janareto kusa da bangaren sashin asusu na gidan gwamnatin.

KU KARANT KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamishinan Ambode ya yi murabus daga APC

Wani ma’aikacin gidan gwamnatin na ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa gobarar ta fara ne da hayaki mai karfi daga tranpoan wnda ya safi dakin janareto.

A wani lamari na daban mun ji cewatsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a ranar Talata, 5 ga watan Disamba ya yi hatsari a gadar Third Mainland da ke jihar Lagas.

Mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Lere Olayinka ya bayyana hatsarin a shafinsa na twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel