Gwamna Nasir El-Rufai yayi alkawarin taimakawa Makauniyar da ta zama Lauya

Gwamna Nasir El-Rufai yayi alkawarin taimakawa Makauniyar da ta zama Lauya

- Gwamna El-Rufai ya gana da Makauniyar da ta zama Lauya a Kaduna

- El-Rufai yayi alkawarin ba Hafsah duk wata gudumuwar da ta ke bukata

Gwamna Nasir El-Rufai yayi alkawarin taimakawa Makauniyar da ta zama Lauya

Baiwar Allah mai fama da larurar makanta ta gana da Gwamna
Source: UGC

Kwanakin baya kun ji labarin yadda wata Baiwar Allah wanda ba ta gani mai suna Hafsah Dauda Sulaiman ta kamalla karatun ta har zama Barista. A wannan makon ne da wannan Baiwar Allah ta gana da Gwamnan Jihar Kaduna.

Hafsah Sulaiman Dauda ta gana da Mai Girma Gwamna Malam Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna har ofishin sa bayan ya ji labarin kwazon ta. Saboda irin wannan cirar tuta da Hafsah tayi, Gwamna El-Rufai da kan sa ya nemi ya gan ta.

KU KARANTA: Babu maraya sai rago: Yadda maras ido ta kammala karatu ta zama Lauya

Gwamna Nasir El-Rufai yayi alkawarin taimakawa Makauniyar da ta zama Lauya

Hafsah da kawar ta a cikin gidan Gwamnatin Jihar Kaduna
Source: UGC

Hafsah Dauda ta ziyarci Mai Girma Gwamnan a ofishin sa ne tare da wata babbar Aminiyar ta, Halima-Sadiya Garba. Malam Nasir El-Rufai yayi alkawarin ba Hafsah duk wata gudumuwa da ta ke bukata domin ta cin ma burin ta.

Legit NG tana da labarin cewa Hajiya Sadiya Garba ita ce ta zama ‘Yar jagorar Hafsah tun farkon shigowar ta Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya har zuwa lokacin da su ka kammala karatu zuwa Makarantar kwarewa a ilmin shari’a.

Hafsah Sulaiman Dauda ta gamu da cutar makanta ne a lokacin tana karamar yarinya. A haka tayi karatun ta na Firamare da Sakandare har ta cin ma burin ta tayi Digiri a bangaren ilmin shari’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel