Ga mai sha'awa: Canada tana bukatar ma'aikata 430,000

Ga mai sha'awa: Canada tana bukatar ma'aikata 430,000

- Wata kungiyar kasuwanci ta yi gargadi kan cewa karanci ma'aikata a kasar Canada na ci gaba da munana, inda a cikin watanni hudu, kasar ke da gurbin aiki har na mutane 430,000

- Karancin ma'aikatan, ya fi shafar bangaren gine gine, noma da kuma fannin danyen mai da iskar gas, hakan kuma yana matukar shafar sauran fannonin aiki a kasar

- Firam Ministan kasar, Justin Trudeau ya ce a halin da kasar take ciki na karancin ma'aikata, akwai bukatar shigowar bakin haure don cike guraben ayyukan

Wata kungiyar kasuwanci ta yi gargadi kan cewa karanci ma'aikata a kasar Canada na ci gaba da munana, inda a cikin watanni hudu, kasar ke da gurbin aiki har na mutane 430,000 a manya da matsakaitun kamfanoni na kasar.

A wani rahoto da hukumar nazari kan harkokin kasuwanci ta kasar Canada mai zaman kanta (CFIB), matakin guraben aiki da ba'a cika ba ya haura zuwa maki 3.3, daga maki 2.9 da yake a shekarar data gabata.

Wannan kuwa "ya haura sakamakon guraben aiki a 2008 wanda kuma ya haddasa durkushewar tattalin arziki, haka zalika 'yan kasuwa na matukar fuskantar kalubale," a cewar Ted Mallet, shugaban sashen tattalin arziki na hukumar CFIB.

KARANTA WANNAN: Babu wata tsiya da mulkin PDP ya tsinanawa Legas a cikin shekaru 16 - Ambode

Firman Ministan kasar Canada, Mr. Justin

Firman Ministan kasar Canada, Mr. Justin
Source: UGC

Karancin ma'aikatan a cewar CFIB, ya fi shafar bangaren gine gine, noma da kuma fannin danyen mai da iskar gas, hakan kuma yana matukar shafar sauran fannonin aiki a kasar.

Wannan rahoton ya zo ne a lokacin da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin Quebec suka dauki matakin janye takunkumi ga shigowar bakin haure.

"Abubuwan da nake ji a fadin Quebec ba ya rasa nasaba da sana'o'i da kuma kasuwanci wanda ake samun karancin ma'aikata, don haka bana tunanin yanzu lokaci ne da zamu rufe shigowar bakin haure, sai bakin haure sun shigo ne zamu samu damar cike guraben ayyukan da muke da su a Canada," a cvewar Firam Ministan kasar, Justin Trudeau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel