2019: Atiku zai garzaya da kamfen dinsa zuwa Arewa ta tsakiya da kudu maso yamma

2019: Atiku zai garzaya da kamfen dinsa zuwa Arewa ta tsakiya da kudu maso yamma

Dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, zai garzaya da kamfen dinsa zuwa yankin arewa maso tsakiya a yau Laraba, 5 ga watan Disamba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa za’a gudanar da gangamin arewa maso tsakiya ne a jihar Kwara.

Ku tuna cewa Atiku ya fara kamfen dinsa a yankin Arewa maso yamma wanda aka gudanar a Sokoto a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba.

2019: Atiku zai garzaya da kamfen dinsa zuwa Arewa ta tsakiya da kudu maso yamma

2019: Atiku zai garzaya da kamfen dinsa zuwa Arewa ta tsakiya da kudu maso yamma
Source: Facebook

An kuma tattaro cewa za’a gudanar da na kudu maso yamma a Ibadan, jihar Oyo a ranar Alhamis, 6 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: BMO ta nemi APC ta haramtawa gwamnonin jam'iyyar 2 yin takarar sanata

Daraktan labarai na kungiyar kamfen din PDP, Mista Kola Ologbondiyan; da kakakin PDP reshen jihar Kwara, Mista Tunde Ashaolu, sun tabbatar da lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel