Boko haram: Buhari ya umarci shugaban hafsoshin sojan sama da ya tare a Borno

Boko haram: Buhari ya umarci shugaban hafsoshin sojan sama da ya tare a Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugaban hafsoshin Sojin rundunar sojan sama, Iya bayis mashal Sadique Abubakar daya tare a jahar Borno don yaki da Boko Haram kamar yadda shugaban hafsoshin rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Buratai yayi.

Idan za’a tuna, a ranar litinin ne ministan tsaro ya bayyana umarnin da shugaba Buhari ya bayar na cewa Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya tattara inasa inasa ya koma jahar Borno har sai zaman lafiya ya inganta a jahar.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Zamfara ta raba ma Sojojin sa-kai Babura 850 don yaki da yan bindiga

Anan ma ministan tsaro, Mansur Dan Ali ne ya bada wannan sanarwa inda yake umartar babban hafsan sojan sama, Sadiqu Abubakar da shima ya tattara tattara inasa inasa ya koma yankin Arewa ta tsakiya don sa ido akan aikin yaki da Boko Haram wanda Sojoji suke yi.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin ministan tsaro, Kanal Tukur Gusau ne a bayyana haka a ranar Talata 4 ga wayan Disamba, inda yace an yanke wannan shawara ne bayan zaman majalisar gudanarwa ta rundunar Sojan sama a karkashin jagorancin Minista Mansur.

“Gwamnati ta umarci babban hafsan Sojan sama ya sabunta dabaru da kuma hanyoyin yaki da yan ta’adda ta yadda zai taimaka ma aikin da Sojojin Operation lafiya dole dake yaki da Boko Haram suke yi a Arewa maso gabas, da aikin sharan daji da Sojoji keyi a Zamfara.” Inji shi.

Daga karshe kanal Gusau ya bayyana cewa a yayin zaman da aka gudanar, hukumar ta amince da karin girma ga wasu manyan hafsoshin Sojoji da suka cancanta zuwa mukami na gaba.

A wani labarin kuma rundunar Yansandan jahar Gombe ta yi ram da wata mata mai shekaru 24, Mariya Yakubu da laifin jefar da danta sabon jariri a cikin wasu rukunin gidaje dake cikin garin Gombe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan Yansandan jahar Gombe, Muhammad Garba Mukaddas ta bayyana cewa Mariya ta jefar da jaririn ne a ranar 24 ga watan Nuwamba a rukunin gidajen Manawashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel