Hadimar Shugaban 'Kasa Buhari ta yada wani rahoto na 'Karya kan Atiku

Hadimar Shugaban 'Kasa Buhari ta yada wani rahoto na 'Karya kan Atiku

Za ku ji cewa allura ta tono garma yayin da adawar siyasa ta sanya hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin hulda da manema labarai, Ms Lauretta Onochie, ta shirga karya kan dan takarar shugaban kasa da jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Ko shakka ba bu hadimar ta shugaban kasa Buhari ta watsa wasu na hotuna kazafi da karairayi a dandalan sada zumunta dangane da al'amurran da suka gudana yayin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP da ya wakana a cikin Birnin Shehu a ranar Litinin din da ta gabata.

A sanadiyar wannan lamari, hadin gwaiwar manema labaran Najeriya karkashin kungiyar Cross Check Nigeria Initiative, ta tona asirin Ms Onochie kan kazafin da ta aikata sakamakon tsantsar adawa ta siyasa da ko kunya ba bu.

Ms Lauretta tare da shugaba Buhari
Ms Lauretta tare da shugaba Buhari
Asali: UGC

Hadimar ta shugaban kasa Buhari cikin rahotonta na kazafi ta yi ikirarin cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP watau Atiku, ya rararaba kudade da kuma abinci yayin yakin neman zabensa da ya kaddamar cikin jihar Sakkwato a jiya Litinin.

Cikin rahoton da ta bayyana a shafin ta na twitter na @Laurestar, Ms Onochie ta watsa wasu hotuna da ta yi ikirarin cewa lamarin da ya wakana kenan yayin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP a birnin Shehu.

Majiyar rahoton jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, bayyanar wannan hotuna karo na farko ta gudana ne tun a watan Fabrairun shekarar 2017 da ta gabata yayin da wata gidauniyar bayar da Sadaka ta gudanar da aikin jin kai a jihar Legas.

Kazalika wannan hotuna sun sake bayyana kwanaki biyu bayan bayyanar su ta farko, a yayin tallata wani Jarumin shirya fina-finan Nollywood da ya kai wata Ziyara Gidan Marayu a watan Fabrairu na shekarar ta shude.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Ku kasance cikin shirin ko ta kwana da jiran tsammani - Hukumar 'Yan sanda ga jami'anta

Kafofin watsa labarai da suka hadar da AFP, The Punch, The Guardian, The Niche da kuma cibiyar kasa da kasa mai gudanar da bincike kan watsa rahotanni, sun tabbatar da wannan kazafi da hadimar shugaban kasa Buhari ta gillatsawa Atiku.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, sake bayyanar wannan hotuna bayan watanni 19 da bayyanar su ta farko, ta dauki hankalin al'umma a zaurukan sada zumunta sai dai Hausawa na cewa 'karya fure take ba ta 'ya'ya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel