Gangamin Atiku: 'Kan mage ya waye' - Sakon matasan Sokoto ga PDP

Gangamin Atiku: 'Kan mage ya waye' - Sakon matasan Sokoto ga PDP

Wasu kungiyoyin matasa karkashin inuwar kungiyar 'Arewa Proactive Youth Coalition' ta yi watsi da kaddamar da kamfen din Atiku a jihar Sokoto tare da bayyana cewar goyon bayan takarar Atiku tamkar shiga tsarin cacar "MMM" ne.

Inuwa Bako, shugaban kungiyar ya musanta ikirarin PDP na cewar taron gangamin ya samu babbar nasara, yana mai bayyana cewar ya kamata jam'iyyar PDP ta san cewar yanzu fa kan mage ya waye, kuma hakan ne ya sa jama'ar da su ka halarci taron basu cika filin wasa mai daukar mutane 10,000 ba.

Bako ya gargadi 'yan Najeriya da su yi hankali da salon yaudara irin na PDP, jam'iyyar da ya ce hatta a fadin alkaluman jama'ar da su ka halarci taron ta sai da tayi karya.

Gangamin Atiku: 'Kan mage ya waye' - Sakon matasan Sokoto ga PDP
Gangamin Atiku: 'Kan mage ya waye' - Sakon matasan Sokoto ga PDP
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

Gangamin jam'iyyar PDP a Sokoto na yankin arewa maso yamma ne, amma abin mamaki sun gaza cika filin wasa mai daukar mutane 10,000, kuma duk da hakan jam'iyyar ba ta ji kunyar sanar da cewar ta samu karfin gwuiwar cin zaben 2019 ba, ta na mai kafa hujja da yawan adadin jama'ar da su ka halarci taron gangamin.

Duk wanda ya yarda da wannan shaci fadi na jam'iyyar PDP, zai iya yarda da tsarin cacar MMM.

"Mutane da gan-gan su ka kauracewa halartar taron PDP saboda sun san babu wani abu sabo dangane da rainin hankalin jam'iyyar da ba su sani ba.

"Jama'ar yankin arewa maso yamma sun fi son su halarci taron gangamin da za su ji maganganu na gaskiya, ma su ma'ana," a cewar Bako.

Shugaban kungiyar ya bukaci jam'iyyar PDP ta jira lokacin da shugaba Buhari zai gabatar da taron gangaminsa a jihar Sokoto da ragowar jihohin arewa domin ganin dumbin jama'ar gaske.

Kazalika, Bako ya caccaki jam'iyyar PDP da Atiku bisa gazawar su na nuna wani muhimmin aiki da su ka yiwa jihar Sokoto a tsawon shekaru 16 da su ka yi a gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel