Zaben 2019 tsakanin barayi da masu gaskiya ne – El-Rufai

Zaben 2019 tsakanin barayi da masu gaskiya ne – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya alakanta zaben 2019 a matsayin takara tsakanin masu gaskia da marasa gaskiya.

El-Rufai wanda ya yi jawabi a taron kaddamar da kungiyar kamfen dinsa a Kaduna ya kuma bayyana kaddamar da kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP wanda aka yi a Sokoto a matsayin taron barayi.

Ya bayyana cewa ya zama dole yan Najeriya su tashi tsaye su nuna cewa Kaduna ba jiha bace da za su bari a cuci mutanensu ba.

Zaben 2019 tsakanin barayi da masu gaskiya ne – El-Rufai

Zaben 2019 tsakanin barayi da masu gaskiya ne – El-Rufai
Source: Depositphotos

“Gaggan barayi sun tattara wuri daya domin yakar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Ina so mutane su sani cewa idan Buhari ya zo Kaduna mutanen Kaduna ne za su tarbe shi ba mutanen wata kasa ba, kuma ina tabbatar muku da haka.”

El-Rufai ya kara da cewa an sami karin sabbin masu zabe har 500,000 kuma karamar hukumar Kaduna ta Arew ne tafi yawan wadannan sabbin masu zabe da mutane akalla 60,000.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC 4 na shirin barin jam’iyyar zuwa AA - Kungiya

Sannan kuma ya hori mambobin kwamitin kamfen din da su garzaya gida-gida, sako-sako, kurdi-kurdi, lungu-lungu, kwararo-kwararo domin ganin an ci gaba da wayar wa mutane kai kan su fito su kada kuria a ranar zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel