Kannywood: Rahama Sadau ta yi murnar samun yawan mabiya miliyan 1 a Instagram
Shahararriyar ‘Yar wasan fina-finan Hausa wato Kannywood da kuma na kudu wato Nollywood Rahama Sadau ta jinjina wa masoyanta da sauran mabiyanta a shafinta na Instagram bayan ta samu cikon mabiya miliyan daya a wannan mako.
Rahama ce mace ta farko a dandalin fina-finan Hausa da ta kai yawan mabiya har miliyan daya.
Hadiza Gabon ce ta ke bi mata da yawan mabiya sama da 800,000 sai kuma jaruma Nafeesat Abdullahi da take da yawan mabiya har 700,000.

Asali: UGC
Tuni dai Rahama ta yi fice a harkar fina-finai duk da cewa ta shigo harkar ne daga baya-baya amma a halin yanzu babu jaruma kamarta da ta ratsa cikin jaruman kudancin Najeriya har da kasashen waje kuma ta yi fice a wannan sana’a.
KU KARANTA KUMA: Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen
A yanzu Rahama ta fada tsundum cikin harkar kasuwanci inda ta kaddamar da kayan shafe-shafe da kwalliya na mata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng