DSS ta gurfanar da matar da ta damfari mutane a fadar Shugaba Buhari

DSS ta gurfanar da matar da ta damfari mutane a fadar Shugaba Buhari

Hukumar DSS ta gurfanar da wata mata mai matsakaicin shekaru, Amina Mohammed wacce aka kuma sani da Justina Onuoha kan zargin shiga fadar shugaban kasa bayan tayi sojan gona a matsayin uwargidan gwamnan jihar Kogi.

Hukumar ta DSS ta kara da cewa matar na shiga cikin fadar shugaban kasa ba tare da izini ba.

Mai Magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunaya, ya ce matar na ta shiga cikin gidan matar shugaban kasa Aisha Buhari.

DSS ta gurfanar da matar da ta damfari mutane a fadar Shugaba Buhari

DSS ta gurfanar da matar da ta damfari mutane a fadar Shugaba Buhari
Source: Facebook

Ya kuma ce ta na ta amfani da sunaye daban-daban domin shiga cikin fadar shugaban kasar.

Sai dai kakakin DSS ya ce ana zargin matar da damfarar wani dan kasuwa naira miliyan 150 a shekarar 2017.

Ya ce ta na amfani da sunan Aisha Buhari wajen damfarar mutane masu neman kwangila a fadar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya fallasa wadanda su ka nemi kujerar sa tun kafin ya bar Duniya – Shehu Sani

Sannan kuma kakakin DSS din ya karyata ikirarin mai laifin na cewa an garkame ta tsawon watanni hudu ba tare da amincewarta ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel