Atiku Abubakar ne zai yi maganin yunwa a Najeriya – Inji Kwankwaso

Atiku Abubakar ne zai yi maganin yunwa a Najeriya – Inji Kwankwaso

A jiya ne Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta kaddamar da shirin yakin neman zaben Shugaban kasa a 2019. Daga cikin wadanda su kayi jawabi a taron akwai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Atiku Abubakar ne zai yi maganin yunwa a Najeriya – Inji Kwankwaso

Kwankwaso yayi kira ga jama’a su fito su zabi Atiku a 2019
Source: UGC

A wajen taron da PDP ta shirya a Garin Sokoto a jiya Litinin 4 ga Watan Disamban 2018, tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi jama’a su zabi Atiku Abubakar a matsayin Shugaban kasa a zaben 2019.

Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa Wazirin Adamawa Atiku ne maganin yunwa a Kasar nan. Kwankwaso ya kuma ce Atiku shi ne wanda zai yi maganin matsanancin rashin aikin yi da ake fama da shi a Yankin Kasar.

KU KARANTA: Buba Galadima ya rantse Atiku zai doke Buhari a zaben 2019

Sanatan na Kano ta tsakiya ya fadawa wadanda su ka halarci taron kamfen din na PDP cewa Atiku Abubakar shi ne wanda zai inganta ilmi tare da kuma gina hanyoyi da asibitoci a fadin kasar nan idan ya samu mulki a zaben 2019.

Har wa yau, Kwankwaso wanda yana cikin wadanda su ka nemi tikitin takarar Shugaban kasa a PDP yayi kira ga mutane maza da mata su marawa Atiku da PDP baya a zaben badi domin habaka harkar gona da taimakon al’umma.

Jiya kun ji cewa Dan takaran PDP Atiku Abubakar ya shawo kan wadanda su ka fusata a Jam’iyyar PDP. Wasu kusohin Jam’iyyar dai sun ji haushin dauko Peter Obi da Atiku yayi a matsayin Abokin takarar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel