Za a binciki yadda aka aiwatar da kwangilar titin Ilorin zuwa Ibadan - Majalisa

Za a binciki yadda aka aiwatar da kwangilar titin Ilorin zuwa Ibadan - Majalisa

Mun samu labari daga NAN cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta soma gudanar da bincike na musamman game da makudan kudin da aka kashe wajen yin aikin hanyar Ibadan zuwa Garin Ilorin.

Za a binciki yadda aka aiwatar da kwangilar titin Ilorin zuwa Ibadan - Majalisa

Kabiru Gaya ya koka da halin da su ka ga samu titin Ilorin
Source: Depositphotos

Kwamitin ayyuka na Majalisar Dattawan Najeriya ya fara bibiyar yadda Gwamnatin Tarayya ta narka kudi har Naira Biliyan 23 wajen gina titin da ya tashi daga Garin Ilorin a cikin Jihar Kwara har zuwa cikin Garin Ibadan a Jihar Oyo.

Shugaban wannan kwamiti, Sanata Kabiru Gaya ya bayyana wannan a Abuja inda yace titin ya sukurkuce gaba daya duk da cewa a 2015 aka kammala aikin. Sanata Gaya ya bayyana cewa da alamun ba ayi wannan aikin da kyau ba.

KU KARANTA: A bayyana wadanda su ka nemi kujerar Osinbajo – inji Sanata Shehu Sani

Babban Sanatan wanda yake wakiltar Kudancin Kano ya tabbatar da cewa za su bi diddikin yadda aka yi wannan aiki tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi. Kabir Gaya yace babu yadda za ayi ace titi ya lalace cikin shekaru 3 kacal da yin sa.

‘Dan Majalisar Dattawan ya koka da cewa akwai rashin gaskiya a lamarin, yana mai shan alwashin ganin an yi abin da ya dace game da titin. Sanatan yace ‘Dan kwangilar yayi watsi da aikin har sai lokacin da ya samu labarin zuwan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel