Tambuwal, Namadi, Makarfi sun baiwa Atiku tabbacin zabubbukan jama'ar Arewa maso yamma
Gwamnan jihar Sokoto, kuma shugaban kamfen Atiku a arewa maso yamma, Aminu Waziri Tambuwal, yace mutanen arewa za su zabi jam'iyyar PDP duk da maganganun ake radawa.
Yayinda yake gabatar da sakon maraba a taron yakin neman zaben kujeran shugaban kasan Atiku Abubakar a Sokoto ranan Litinin, Tambuwal yace yan Najeriya sun dade suna jiran kwararren mutum wanda zai shugabancesu.
Yace: "Idan aka zabi Atiku, zai kawo sauyi bangaren aikin noma, ilimi, samar da aiki yi ga matasa da tabbatar da bin doka da oda."

Asali: Facebook
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon minista, Kabiru Tanimu; tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo; sun bukaci mutanen yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Asali: Facebook
Mun kawo muku rahoton cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da wasu manyan mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun bi sahun dubban masoya a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba, a Sokoto don kaddamar da kamfen din arewa maso yamma na dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng