Yara 19 sun mutu bayan jirgin ruwa ya kife da su a Kwara

Yara 19 sun mutu bayan jirgin ruwa ya kife da su a Kwara

Mun samu rahoton cewa a kalla yara 19 ne suka mutu a rafin Niger yayin da jirgin ruwan da ke dauke da su ya kife a ranar Asabar a Lafiagi da ke karamar hukumaer Edu na jihar Kwara.

Daily Trust ta ruwaito cewa suna hanyarsu na zuwa hallartar wani daurin aure ne a wani gari a jihar Niger.

Wani majiya ya ce jirgin ruwan yana dauke da mutane 22 ne kuma mafi yawancinsu yara ne yayin da ya kife, majiyar ya ce yara 19 sun mutu yayin da guda biyu suka tsira da ransu.

Yara 19 sun mutu bayan jirgin ruwa ya kife da su a Kwara
Yara 19 sun mutu bayan jirgin ruwa ya kife da su a Kwara
Asali: Original

"A yammacin Asabar, an ciro gawarwarkin mutane hudu daga rafin. An sake komawa a ranar Lahadi domin kokarin gano gawarwakin sauran.

DUBA WANNAN: Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

"Jami'an 'yan sanda da na Kwana-kwana sun zo a jiya domin taimakawa wajen ceto yaran amma dai mutane biyu ne kawai aka ceto ransu," inji majiyar.

Alhaji Suleiman Aliyu, sakataren masarautar Lafiagi ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Aliyu ya ce a yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda hatsarin ya ritsa da su ba inda ya ce mutane na fadin maganganu mabanbanta.

"Tabbas sun kai 12. Adadinsu na tsakanin 12 ne zuwa 19 kamar yadda ka daga," kamar yadda ya shaidawa majiyar Legit.ng

Jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar, DSP Ajayi Okasanmi shima ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin wadanda hatsarin ya ritsa da su ba saboda har yanzu ana kokarin ceto su.

A bangarensa, Gwamna Abdulfatah Ahmed ya mika ta'azziyarsa ga Sarkin Lafiagi, Alhaji Saadu Kawu Haliru game da rasuwar yaran.

Muhimmiyar sanarwa: : Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel