Ashsha! Motar daukan kaya ta kufce ma direba, ta tattake mutum 10 har lahira

Ashsha! Motar daukan kaya ta kufce ma direba, ta tattake mutum 10 har lahira

Mutuwa daya ce, amma sanadinta da yawa, inji Malam Bahaushe, haka zalika ko a cikin addinin Musulunci an bayyana mana cewa babu wata rai data san ranar mutuwarta, wannan shine kwatankwacin lamarin daya faru da wasu yan kasuwa guda goma a Jega.

Wata motar daukan kaya a cikin garin Jega na karamar hukumar Jega ta kwace daga hannun direban, inda ta yi kan wasu yan kasuwa su goma dake sana’ar saye da sayarwa a gefen titi, ta tatattakesu har lahira, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta zargi an sace naira tiriliyan 11 a gwamnatin APC ta Buhari

Wani shaidan gani da ido, Mallam Adamu Jega ya bayyana cewa motar ta fito ne daga yankin Yauri/Koko a lokacin da ta kwace ma direban a daidai lokacin dayake kokarin kauce ma wata karamar mota da ta yi gaba da gaba da shi.

Bugu da kari da yake lamarin ya faru ne a gab da kasuwa, kaucewarta keda wuya sai tayi kan yan kasuwan dake gefen hanya, inda nan take ta kashe mutane goma, yayin kimanin mutane arba’in da shida suka jikkata.

Majiyar Legit.com an garzaya da wadanda suka samu rauni daban daban zuwa babban asibitin karamar hukumar Jega don basu kulawar da ta dace, duba da mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Haka zalika wani shaidan gani da ido, Mallam Yusuf Muhammad ya bayyana cewa “Allah ya kiyaye da an samu gawarwaki da yawa, sai dai dayake jama’a sun hangi motar tun daga nesa suka tsetstsere shine abin yazo da sauki a haka.”

Sai dai koda majiyarmu ta tuntubi kaakakin hukumar kare haddura ta kasa reshen jahar Kebbi, Ibrahim Kangiwa don jin ta bakinsa, sai yace gaskiya har zuwa lokacin ba samu rahoton hatsarin ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: