Obasanjo ya rubuta wasika zuwa ga shugaba Trump na Amurka

Obasanjo ya rubuta wasika zuwa ga shugaba Trump na Amurka

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya rubutawa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, wasikar ta'aziyyar tsohon shugaban kasar Amurka, George H. W Bush.

A takardar ta Obasanjo da Kehinde Akinyemi, mai taimaka masa a bangaren yada labarai, ya nunawa manema labarai, tsohon shugaban kasar ya ce samun labarin mutuwar Bush a ranar Juma'a ya matukar girgiza shi.

Ya bayyana marigayin da cewar shugaba ne da ya kawo canji ta fuskar canja alkiblar alakar kasashen Afrika da kasar Amurka.

Obasanjo ya rubuta wasika zuwa ga shugaba Trump na Amurka
Obasanjo ya rubuta wasika zuwa ga shugaba Trump na Amurka
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki

"Ba iya iyalin Bush da 'yan uwansa da kasar Amurka ne kawai zasu ji zafin mutuwar sa ba, duniya bakidaya ta yi babban rashi. Nasarorin da ya kawo ta fuskar kyautata alaka tsakanin kasashen duniya, tabbatar da dorewar dimokradiyya, da kulla alakar kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da Amurka, za su cigaba da tuna mana da shi," a cewar Obasanjo a cikin wasikar ta sa.

"Marigayi Bush masoyin Najeriya ne, mulkinsa ne silar kulluwar kyakykyawar alaka tsakanin Najeriya da kasar Amurka. Muna taya Amurka rashin jarumin dattijo, masanin makamar aiki," kamar yadda Obasanjo ya fada a cikin wasikar sa.

Obasanjo ya kara da cewar rayuwar Bush za ta cigaba da zama a bar koyi ga duk ma su son kawo canji ta hanyar hidimtawa kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel