Hotunnan wata dattijuwa mai shekaru 95 da ta shiga makarantar firamare

Hotunnan wata dattijuwa mai shekaru 95 da ta shiga makarantar firamare

Masu iya magana sukan ce gemu dai baya hana neman ilimi. Wannan karin maganar ya yi dai-dai da abinda ya faru a rayuwarta wata dattijuwa da ta bai wa mutane mamaki sosai yayin da ta koma makaranta duk da tsawon shekarunta.

Wata dattijuwa 'yar kasar Kenya, Chebelina mai shekaru 95 da bawa mutane mamaki bayan hotunan ta sanya da kayen makaranta ya bazu a kafafen sada zumunta na zamani da wasu kafafen watsa labarai.

Hotunnan wata dattijuwa mai shekaru 95 da ta shiga makaranta

Hotunnan wata dattijuwa mai shekaru 95 da ta shiga makaranta
Source: UGC

DUBA WANNAN: An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki

A cewar wani wata amfani da Instagram, Wanjiku Kinuthia, mai magana da yawun wani kamfanin kula da gandun daji, ta bayyana cewa labarin Chebelina ya bazu ne a Kenya bayan hotunan ta sanye da kayan maranta a cikin aji ya bazu.

Wani sako da aka wallafa a Facebook ya ce: "Sunan ta Chebelina Mukomuga. Ta yi kiyasin cewa an haife ta a shekarar 1923 kuma abinda ta aikata ya nuna cewa tsufa ba dalili bane da zai hana mutum cimma abinda ya ke son yi a rayuwa, misali koyon rubutu da karatu."

A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumunta mai suna @Ofentse_magqoki yayin da ta ke bayyana farin cikin ta bayan kammala karatun digirinta. Kyakyawar budurwar ba ta amince wani abu ya hana ta cimma burinta ba duk da cewa ta kwashe shekaru shida kafin kammala karatun da ya kamata a gama a shekaru hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel