Yanzu Yanzu: Yan majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun

Yanzu Yanzu: Yan majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun

Yayinda yan Najeiya ke shirin zaben 2019, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Ogun ta rasa akalla mambobinta sama da 26 a majalisar dokokin jihar inda suka koma jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Masu sauya shekar sun kasance fusatattun yan takara, wadanda ke zargin cewa shugaban jam’iyyar mai mulki ya sace kuri’un da suka samu a lokacin zaben fidda gwani da aka yi a ranar 7 ga watan Oktoa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Ya majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun
Yanzu Yanzu: Ya majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa daya daga cikin masu sauya shekar, Lamidi Olatunji ya bayyana cewa sun yanke shawarar kaddamar da kudirinsu a APM.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi namijin kokari, ya cancanci yin tazarce – Abdullahi Adamu

Sun kuma yaba ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan jajircewa da yayi wajen ganin an shawo kan matsalar da APC reshen Ogun ke ciki.

Daga cikin masu sauya shekar akwai kwamishinoni biyu masu ci Dayo Adeneye (labarai da tsare-tsare) da Modupe Mujota (ilimi, kimiya da fasaha).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel