Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta aika sammaci ga jakadan Amurka

Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta aika sammaci ga jakadan Amurka

Majalisar dokokin Najeriya ta aika sammaci ga jakada kasar Amurka a Najeriya, Mista Stuart Symington kan zargin hana yan Najeriya da yawa biza.

Gayyatar ya biyo ban wani korafi da lauya mai kare hakkin jama’a, Kayode Bello ya aike ma majalisa kan lamarin.

Jaridar Punch ruwaito cewa ta gudanar da bincike kan yadda aka hana dalibai yan Najeriya da dama da ke neman karatu a makarantun Amurka biza duk da kashe kudade da dama da suka yi akai.

Kudaden sun had daga na biza da makaranta, kuma sannan ance ba’a dawo da kudin idan har mutun ya rigadaya biya.

Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta aika sammaci ga jakadan Amurka

Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta aika sammaci ga jakadan Amurka
Source: Depositphotos

Yayinda wasu dalibai suka yi kirarin cewa an hana masu biza saboda basu da aure, wasu sunce an hana su ne saboda mutun daya daga cikin iyayensu ne ya dauki nauyin.

Wasu iyaye sunyi ikirarin cewa an katse hira da ýarsa don kawai ta nemi mai yi mata tambayan ya daga murya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ya majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun

An tattaro cewa za’a fara zaman ne a ranar Talata, 4 ga watan Disamba da misalin karfe 2pm a majalisar wakilai daki na 429.

Magatakardan majalisar, Mista Omale Adoyi ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba.

Sannan yace ofishin jakadancin Amurka sun yi watsi da sammacin. Inda ya kara da cewa dole a dage zaman idan har suka ki bayyana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel