Buhari ya yi namijin kokari, ya cancanci yin tazarce – Abdullahi Adamu

Buhari ya yi namijin kokari, ya cancanci yin tazarce – Abdullahi Adamu

Sanata mai wakiltan yankin Nasarawa ta yamma a majalisar dokokin kasar, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika dukkanin alkawaran zaben da ya dauka tare da habbaka tattalin arziki tsaro da kuma yaki da rashawa.

Ya bayyana hakan a jiya a Keffi, jihar Nasarawa a lokacin taron karrama Dr Samson Adewale Adegoke wanda yayi ritaya a matsayin daraktan kudi da asusu, cibiyar lafiyar tarayya, wanda kungiyar matasan Keffi suka shirya.

Buhari ya yi namijin kokari, ya cancanci yin tazarce – Abdullahi Adamu

Buhari ya yi namijin kokari, ya cancanci yin tazarce – Abdullahi Adamu
Source: UGC

Sanata Adamu, ya ce gwamnatin Buhari ta kawo ci gaba sosai ga rayuwar yan Najeriya ta hanyar habbaka tattalin arziki, da kuma magance rashawa tare kuma da kare rayuka da dukiyar jama’a.

KU KARANTA KUMA: Allah na da wani sako ga Najeriya - Osinbajo

Ya bukaci yan Najeriya da sake zabar shugaba Buhari a 201 domin ya samu damar kammala dukkanin kyawawan ayyukan da ya fara.

A baya mun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan ya ambaci sunayen wadanda suka nemi Yemi Osinbajo ya nada su a matsayin mataimakin shugaban kasa a lokacin das hi Buhari) ke jinyar rashin lafiya.

Sani wanda ke martani ga ikirarin shugaba Buhari na cewa wasu mutane sun zata ya mutu ne a lokacin da yake jinya a 2017, ya ce yana tsoron kan idan ba’a bayyana sunayen makisan ba yanzu sai yan Najeriya sun tsaya jiran tsammani na tsawon shekaru kafin a gano mutanen a littafin shugaban kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel