Qatar ta yi wa Kasar Saudi bore ta janye kan-ta daga tafiyar OPEC

Qatar ta yi wa Kasar Saudi bore ta janye kan-ta daga tafiyar OPEC

- Kasar Qatar za ta fice daga cikin Kungiyar OPEC a farkon shekarar 2019

- Ministan harkokon mai na Kasar ne ya bayyana wannan a wajen wani taro

- Qatar tace wannan mataki dai da ta dauka bai da alaka da lamarin siyasa

Qatar ta yi wa Kasar Saudi bore ta janye kan-ta daga tafiyar OPEC
Kasar Qatar tana hako gangar mai 600, 000 a kowace rana
Asali: Depositphotos

CNBC ta rahoto cewa Ministan harkokin man fetur na kasar Qatar ya bayyana cewa za su fice daga cikin Kungiyar nan ta kasashen da ke hako danyan mai watau OPEC. Kasar Qatar za ta bar Kungiyar ne a farkom Junairun 2019.

Saad Al-Kaabi wanda shi ne Ministan main a Kasar ya bayyana wannan a Ranar Litinin dinnan a wajen wani babban taro da aka shirya. Kasar ta Qatar ta dauki wannan mataki ne bayan ta gana da masu harkar man fetur a Kasar.

Ministan na Qatar yayi kokarin nuna cewa Kasar ta dauki wannan mataki ne domin nemawa kan ta masalaha. Saad Al-Kaabi yace ficewa daga Kungiyar ba ta da alaka ko nasaba da harkar siyasar Yankin Gabas ta tsakiyar Duniya.

KU KARANTA: 'Yar takarar Shugaban kasa tayi alkawarin samar da lantarki a Najeriya

Qatar dai ba ta cikin manyan Kasashen da ke kan gaba wajen harko fetur a Duniya, sai dai Kasar ta na da dinbin arziki musamman na gas. Yanzu haka dai Saudi-Arabia wanda ita ce gaba a cikin tafiyar OPEC ba ta shiri da Qatar.

Kasar Saudi da sauran ‘Yan kanzagin ta a Yankin Larabawa sun makawa Qatar takunkumi saboda wata takkadama kwanakin baya. Wannan mataki da Lasar Qatar ta dauka ya ba jama’a da-dama mamaki kwarai da gaske inji ‘Yan jarida.

Duk da farashin gangar man fetur yana yin kasa kwanan nan, masana sun ce ficewar Qatar din ba zai yi wani tasiri sosai ba. Daga Watan Oktoba zuwa yanzu dai farashin man yana kara yin kasa a kasuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel