Karanbatta tsakanin kungiyoyin matsafa ya yi sanadin halaka wani kasurgumi dan ta’adda

Karanbatta tsakanin kungiyoyin matsafa ya yi sanadin halaka wani kasurgumi dan ta’adda

Wani fitaccen dan kungiyar asiri da ya yi kaurin suna a garin Oshogbo na jahar Osun da aka fi sani da suna da Badoo ya gamu da ajalinsa a hannun wasu yayan kungiyar asiri dake hamayya dasu, kamar yadda jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito an kashe Badoo ne a wata matattarar mashaya ta Star Night dake gab da ofishin jam’iyyar APC na unguwar Ladsol a cikin garin Osogbo, inda abokan gaba suka fi karfinsa a fadan daya kaure tsakanin kungiyarsa da kungiyarsu.

KU KARANTA: Wa’iyazubillahi: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga jigon APC saboda laifin wulakanta Al-Qur’ani

Wannan arangama da aka yi tsakanin yayan kungiyoyin asirin ya tayar da hankulan jama’a mazauna yankin, inda suka kai rahoto ga rundunar Yansandan jahar wanda ta tura jami’anta zuwa yankin don shawo kan matsalar.

Kwamishinan Yansandan jahar Osun, Fimihan Adeoye ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya tabbatar da kisan dan ta’adda Badoo, a cikin wata hira da ya yi da majiyarmu inda ya bayyana cewa a yanzu hankula sun kwanta.

“Eh, an kashe mutum daya a yayin rikici tsakanin kungiyoyin asiri guda biyu, a yanzu haka mun kaddamat da bincike game da lamarin, hankula sun kwanta, amma bamu kama kowa ba a yanzu, kuma ina tabbatar muku zamu kama duk masu hannu cikin rikicin.” Inji shi.

Rahotanni sun bayyana cewa Yansanda sun sha kama Badoo kan laifuka da dama da suka danganci kisan kai, fashi da makami da sauran miyagun laifuka, amma a duk lokacin da suka kamashi suka mikashi gaban kotu, sai kotu ta sake shi, ya dawo kuma ya sake maimaita wani danyen aiki.

Har yanzu dai jama’an unguwar na zaune cikin halin dar dar don tsoron kada yaran Badoo su sake komawa unguwar da nufin daukar fansa ta hanyar kai hare haren ramuwar gayya wanda yawanci yana karewa ne akan jama’an da basu ji ba, basu gani ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel