Dansadau ya fara kamfen, ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu a Zamfara

Dansadau ya fara kamfen, ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu a Zamfara

Dan takarar kujeran gwman a karkashin inuwar jam’iyyar National Rescue Movement (NRM) a jihar Zamfara, Sanata Sa’idu Dansadau, ya yi alkawarin kawo karshen fashin shanu da rashin aiki idan har aka zabe shi a zabe mai zuwa.

Dansadau ya yi alkawarin yayinda yake fara kamfen dinsa na neman kujerar gwamna a jiya Lahadi, 2 ga watan Disamba a Gusau.

Zirga-zirgan ababen hawa a hanyar Funtua-Gusau ya samu tsaiko na dan wani lokaci sakamakon jerin gwano da motocin magoya bayan NRM suka yi a yayinda suke wad an takarar gwamnan maraba da dawowa gida.

Dansadau ya fara kamfen, ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu a Zamfara

Dansadau ya fara kamfen, ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu a Zamfara
Source: UGC

Dansadau ya samu rakiyar yan takarar gwamnan jam’iyyar na jihohohin Sokoto, Kano da Katsina da kuma yan takarar sanata da sauransu.

Magoya bayan nasa na ta wakar “Ba ruwan mu da barayin shanu” wanda hakan hannunka mai sanda ne da gwamnatin APC a jihar.

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

Dansadau ya bayyana muhimman abubuwa uku da gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen yi a jihar wadanda suka hada da, yaki da rashin tsaro, samar da ayyukan yi da kuma ilimi.

Ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu da yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel