Jam’iyyar APC ta rasa wasu jiga-jigan ‘Yan Majalisa a Bauchi

Jam’iyyar APC ta rasa wasu jiga-jigan ‘Yan Majalisa a Bauchi

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta rasa wasu ‘Ya ‘yan ta a Jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya. Wadanda su ka bar Jam’iyyar, sun tattara ne sun koma PRP.

Jam’iyyar APC ta rasa wasu jiga-jigan ‘Yan Majalisa a Bauchi
Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji M. A Abubakar
Asali: UGC

Daga cikin wadanda su ka sauya-sheka daga APC akwai Mataimakin Kakakin Majalisar dokokin Jihar Bauchi, Abdulmumini Bala Fanti da wasu ‘Yan Majalisar Jihar 2. Yanzu haka dai Jam’iyyar adawa ta PRP tana ta kar karfi a Kasar.

Sauran ‘Yan Majalisar da su ka fice daga APC din su ne: Ibrahim Bello Katagum da kuma Yusuf C. Nuhu. Kwanan nan ne ma Hon. Yusuf Nuhu wanda ke wakiltar Toro a Majalisar dokoki ya lashe zabe zuwa Majalisar Wakilai ta Tarayya.

KU KARANTA: Jam’iyyar PRP tana karfi a Jihar Kano bayan ficewar 'Dan takaran Gwamna a PDP

Har wa yau, Barista Lawan Ibrahim wanda ya nemi kujerar Sanatan Jihar a karkashin APC ya tattara ya koma PRP. Wani ‘Dan Majalisar dokokin Jihar da ke harin kujerar Majalisar Tarayya, Yakubu Shehu Abdullahi ya bi sahun su.

Kafin nan dama wanda ya nemi kujerar Gwamna a APC, Mohammed Ali Pate yana cikin wadanda su ka koma Jam’iyyar ta PRP tuni. Shugaban Jam’iyyar ta PRP a Jihar Bauchi, Alhaji Shehu Barau Ningi ya tabbatar mana da wannan jiya.

Mun tambayi wani tsohon ‘Dan Majalisar Jihar kuma wanda ya nemi kujerar Sanata a APC amma bai samu ba, Aliyu Ibrahim Gebi game da batun tserewa daga APC inda ya tabbatar da cewa har yanzu yana tare da Jam’iyyar mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel