Za a kwata: Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta yi barazanar shiga yajin aiki

Za a kwata: Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta yi barazanar shiga yajin aiki

Kungiyoyin 'yan kasuwar man fetur sun bawa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 7 don ta biya su bashin kudin tallafin man fetur kimanin biliyan N800bn da su ke bi ko su daka yajin aiki.

Duk da kasancewar kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) ne ke da alhakin sayo man fetur daga kasashen ketare, ta dogara ne da ma'adanan 'yan kasuwa domin ajiya da raba man fetur a fadin kasar nan. Hakan na nufin za a fuskanci wahalar mi idan 'yan kasuwar su ka rufe ma'adanansu na man fetur.

Kungiyoyin da ke cikin barazanar tafiya yajin aikin sun hada da MOMAN, DAPPMA da kuma IPPIs.

Da su ke tabbatar da barazanar shiga yajin aikin matukar gwamnati ba ta biya su kudin da su ke nema ba, Patrick Etim, mai bawa kungiyar IPPI shawara a bangaren shari'a, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar dukiyar 'yan kasuwar na nema karewa a hannun bankunan kasar nan saboda yawan bashin kudin da ake binsu.

Za a kwata: Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta yi barazanar shiga yajin aiki

Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta yi barazanar shiga yajin aiki
Source: Depositphotos

A cewar Etim, 'yan kasuwar ba su da wani zabi da ya wuce su umarci ma'aikatansu su zauna a gida har sai gwamnati ta biya su dukkan kudaden tallafin da su ke bi.

"Hanya daya tilo da za ta hana kungiyar 'yan kasuwar man fetur shiga yajin aiki shine gwamnati ta biya su madarar kudaden da su ke bi, ba takardar alkawari ba.

"Har yanzu gwamnati ba ta yi komai ba a kan biyan 'yan kasuwar duk da alkawarin da ta dauka a watannin baya," a cewar Etim.

DUBA WANAN: Rundunar sojin sama ta yi gwajin dabarun ceton rai daga samaniya

Ya kara da cewar gwamnatin shugaba Buhari ta biya wani bangare na kudaden da 'yan kasuwar ke bi bashi amma duk da haka akwai ragowar kudi ma su nauyi da su ke bin gwamnati.

Ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ba ta mayar da wani martani game da wannan barazana ta 'yan kasuwar man fetur ba.

Wahalar man fetur a karshen shekara ba sabon abu ba ne a Najeriya. Sai dai bayan wahalar man fetur a karshen shekarar 2017, gwamnatin tarayya karkashin shugaba Buhari ta ci al washin cewar ta shawo kan matsalar har abada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel