Ya kamata a daina nada tsofaffin mutane a matsayin Ministoci - Gbor

Ya kamata a daina nada tsofaffin mutane a matsayin Ministoci - Gbor

Mun ji cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APGA, Janar John Gbor yayi hira da Jaridar Vanguard kwanan nan inda ya bayyana shirin da yake da shi inda ya karbi mulkin kasar nan a 2019.

Ya kamata a daina nada tsofaffin mutane a matsayin Ministoci - Gbor

‘Dan takarar APGA yace ya kamata a horas da Sojoji a canza hafsoshi
Source: UGC

Manjo Janar John Gbor ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari ya gaza kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya. Tsohon Janar din yace an san Sojojin Najeriya da kokari a ko ina a fadin Duniya amma sun gaza kashe wutar Boko Haram.

‘Dan takarar yace Shugaba Buhari bai ba Hafsun Sojojin kasar umarnin da ya dace wajen kawo karshen rikice-rikicen da ake yi a Najeriya ba. Gbor yace ya kamata a horas da Sojojin kasar yadda ya kamata idan har a nan matsalolin su ke.

KU KARANTA: Abin da zan yi cikin shekaru 4 idan na koma kan mulki – Buhari

John Gbor ya bayyana cewa idan har Janar din da ke jagorantar Sojojin kasar ya gaza kai Najeriya ga nasara, abin da ya dace ayi shi ne Shugaban kasa Buhari ya canza sa. Haka kuma yace jama’a su canja Buhari a zaben 2019 saboda gazawar sa.

A hirar, ‘Dan takarar Shugaban kasar ya nuna cewa zai hada-kan ‘Yan Najeriya kamar yadda Janar Yakubu Gowon yayi a lokacin yana kan mulki lokacin da yakin Basasa ya barke. Gbor yace akwai matsalar rashin yadda da juna a fadin Kasar nan.

Gbor yace zai tafi da Matasa idan har ya samu mulkin kasar nan a 2019 inda yace har yanzu tsofaffin da su kayi mulki ne tun 1960 ake cigaba da nadawa a Gwamnati. Gbor yace Gwamnatin nan ta Shugaba Buhari tayi watsi da Matasa da su kayi karatu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel