Matashi dan shekara 16 ya kashe budurwarsa saboda ta fara soyaya da yayansa

Matashi dan shekara 16 ya kashe budurwarsa saboda ta fara soyaya da yayansa

Wani matashi mai suna Idrisu Muhammadu ya kashe budurwarsa, Fatima Isah saboda tayi watsi da soyayarsu ta koma soyaya da yayansa.

Lamarin ya faru ne a kauyen Evutagi a karamar hukumar Katcha na jihar Niger.

Marigayiyar, Fatima mai shekaru 32 ta fadawa Idrisu cewa ba za ta iya aurensa ba saboda ya yi mata yaranta hakan ya sa ta fara soyaya da yayansa.

A hirar da ya yi da The Nation, Idrisu ya amsa cewa shi ne ya kashe Fatima amma kafin hakan ya dade yana fama da yayansa kan cewa shine ya dace ya aure ta.

Zafin soyaya: Dan shekara 16 ya kashe budurwarsa saboda ta fara soyaya da yayansa

Zafin soyaya: Dan shekara 16 ya kashe budurwarsa saboda ta fara soyaya da yayansa
Source: Depositphotos

Ya yi bayyanin cewa kishi ne ya sanya shi ya kashe Fatima da adda yayin da yayansa da ke tare da ita a lokacin da tsere domin ya tsira da rayuwarsa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto

Idrisu said: "Na fadawa yaya na ya kyale min Fatima saboda na riga na fada mata ina son in aure ta amma bai kyale ta. A ranar da abin ya faru, na gansu tare kawai sai zuciya ta debe ni kuma na kashe ta.

"Yanzu ga abinda ya faru nan, na aikata kisa kuma zan kare rayuwa ta a gidan yari tun ina shekara 16. Idan da na sani, da na kyale Fatima tunda ba a aure dole. Idan ba sa'a nayi ba, za a yanke min hukuncin kisa kuma in dawamma a wuta saboda na nemi in karbi abinda ba nawa ba," inji Idrisu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammad Abubakar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shine ya kashe marigayiya Fatima.

"Wanda ake zargin ya kwashe shekaru uku yana yiwa Fatima barazana amma abin takaici babu wanda ya dauki mataki a kai, yanzu ga abinda ya faru," inji Abubakar.

Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya idan an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel