Ba ni da laifi kan sace 'Yan Matan Chibok - Jonathan

Ba ni da laifi kan sace 'Yan Matan Chibok - Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana cewa a akwai nau'in damuwa a zukatan al'ummar kasar dangane da rashin daidaituwa a tsakankanin hukumomin kasar nan ma su ruwa da tsaki kan harkokin gudanar da zabe na 2019.

Sai dai tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa, yana da cikakken yakini da kuma aminci kan hukumar zabe ta kasa, hukumar 'yan sanda, hukumar dakarun sojin kasa da kuma hukumar 'yan sandan fararen kaya ta DSS.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na BBC inda ya kuma bayyana cewa, ba ya da wani alhaki kan sace 'yan Matan Chibok cikin jihar Borno a watan Afrilun shekarar 2014.

Dangane da wannan lamari kungiyar ta'adda ta Boko Haram da ta sace fiye da Dalibai 200 na Makarantar Mata da ke garin Chibok, Dakta Jonathan ya bayyana cewa ba ya da laifi duk kasancewarsa shugaban kasa a wannan lokaci.

Dakta Jonathan ya bayyana cewa, alhakin wannan lamari yana rataye a wuyan wadanda suka aikata ta'addancin shekaru kimanin biyar da suka gabata domin kuwa kasancewar sa shugaban kasa na wannan lokaci ba ya da hurumin fita filin daga inda za a fafata tare da shi.

KARANTA KUMA: Lamarin Atiku na neman izinin shiga kasar Amurka abu ne na sirrance - Jakadan Amurka

Tsohon shugaban kasar yayin zayyana wannan batutuwa kan wannan lamari na sace 'Yan Matan Chibok ya kuma bayyana cewa, akwai wani kaso na amincewarsa dangane da yadda kwazon gwamnatinsa bai haifar da wani tasiri ba na dakile aukuwar lamari gami da ceto 'yan Matan bayan aukuwar sa.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Tsohon shugaban kasa Jonathan ya bayyana takaicinsa dangane da yadda aka siyasantar da lamarin sace 'Yan Matan Chibok a nan gida Najeriya da kuma kasashen duniya da ketare.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel