Dan majalisa ya zargi kungiyoyi masu zaman kansu da tallafa wa Boko Haram

Dan majalisa ya zargi kungiyoyi masu zaman kansu da tallafa wa Boko Haram

Wani mamba na majalisar wakilai mai wakiltan yankin Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi na jihar Jigawa, Gudaji Kazaure ya zargi wasu kungiyoyi masu zaman kansu da taimakawa yan ta’addan Boko Haram.

Mista Kazaure wanda ya kasance dan kashenin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan a wani hira da jaridar Premium Times a majalisar dokokin kasar.

Da farko dai jaridar Premium ta ruwaito yadda yan ta’addan Boko Haram suka kashe kimanin sojojin Najeriya 118 a ranar 18 ga watan Nuwamba a kauye Metele, jihar Borno. Amma dai rundunar ta ce sojoji 23 kawai aka kashe.

Dan majalisa ya zargi kungiyoyi masu zaman kansu da tallafa wa Boko Haram

Dan majalisa ya zargi kungiyoyi masu zaman kansu da tallafa wa Boko Haram
Source: UGC

Yayinda yake mayar da martani ga kisan sojiji a Metele, Mista Kazaure yayi zargin cewa kungiyoyin jama’a na taimakawa yan ta’addan da kayyayakin agaji a filin daga.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Buratai ya bukaci dakarun soji da su dauki yanayi mai tsauri

Sai dai Kazaure bai bayyana kowacce kungiyar agaji da yake zargi da aikata hakan ba don marawa zarginsa baya.

Dan majalisan ya kuma yi zargin cewa da alamu babu hadin gwiwa tsakanin rundunar sojin Najeriya da sojin sama, cew rundunar sojin sama na samun umurni ne daga hedkwatar ta na Abuja.

Ya nace kan cewa lallai shi da sauran yan farauta za su iya shiga daji su kara da yan ta’addan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel