Jami’an hukumar yan sanda Najeriya sun hallaka yan baranda 104, sun damke 85

Jami’an hukumar yan sanda Najeriya sun hallaka yan baranda 104, sun damke 85

Hukumar yan sandan Najeriya ta alanta cewa jam’anta sun hallaka yan taki zama 104 a wani mumunan hari da suka kai dajin Mahanga dake karamar hukumar Birnin Mogaji a jihar Zamfara.

Jawabin da kakakin hukumar, DCP Jimoh Moshood, da ya saki a ranan Juma’a ya ce an tawarwatsa mabuyar yan baranda 50 a sansani uku.

DCP Jimoh Moshood ya kara da cewa an kwato shanaye 500 da tinkiyoyi 79 daga hannunsu, kana an rasa jami’an dan sanda daya a harin.

Yace bisa ga kasha-kashen da ke faruwa a jihar, sifeto janar na hukumar yan sanda a ranan 9 ga watan Nuwamba, ya tura jami’an yan sanda 1,000.

Rundunar 'yan sanda ta maidawa jam'iyyar APC martani kan bukatar da ta gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na tsige Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda (IGP) kafin babban zabe na 2019.

KU KARANTA: Daga dawowa daga Chadi, Shugaba Buhari zai tafi kasar Poland gobe Asabar

A ranan Alhamis, jami'in hulda da jama'a na rundunar, Mr Jimoh Moshood, ya yi watsi da wannan zarge-zargen da jam'iyyar PDP ta gabatar akan Sifeta Janar din, na cewar yana da sauyin sauya akala musamman idan akazo batun zabe.

Ya kuma bayyana wannan kira da PDP ta yi na Sifeta Janar din ya rubuta takardar murabus daga kujerarsa da kansa a masatin wani wasan yara da ya kamata ayiwa dariya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel