Wa’iyazubillahi: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga jigon APC saboda laifin wulakanta Al-Qur’ani

Wa’iyazubillahi: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga jigon APC saboda laifin wulakanta Al-Qur’ani

Lahaula wala kuwwata illa billahi, irin wannan rayuwa da ake bukatar mutane su yi taka tsantsan a wajen neman duniyarsu ta yadda lahira za ta yi musu kyau, amma sai kaga wasu mutanen da kansu suke neman halaka, halaka duk inda take sai sun nemota.

Anan wani jigo a jam’iyyar APC, kuma tsohon shugaban jam’iyyar a sabongarin Gusau, babban birnin jahar Zamfara ne ya wulakatan littafi mai tsarki na addinin Musulunci, watau Al-Qur’ani mai girma, inda yayyaga shi, ya kekketa shi tare da yin wurgi da shi.

KU KARANTA: Korarrun ma’aikatan jahar Kaduna sun shiga hannu bayan an kamasu suna yi ma El-Rufai Al-kunut

Wa’iyazubillahi: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga jigon APC saboda laifin wulakanta Al-Qur’ani
Mainasara
Asali: Facebook

Wani karin abin bacin rai game da wannan lamari ta yadda zaka fahimci da gangan wannan makirin mutum yayi wannan aika aika shine daya kekketa Al-Qur’anin, sai ye jefa shi cikin masai, innalillahi wa inna ilaihi rajiun!

Duk wannan maganan da ake yi fa, mutumin da ya aikata wannan babban laifi Musulmi ne, sunansa Mainasara Mansur, shahararren dan siyasa musamman a cikin jam’iyyar APC, tare da wani abokinsa, kamar yadda wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Sani Yawuri ya bayyana.

Majiyar Legit.com ya bayyana cewa Mainasara da abokinsa sun aikata wannan laifi ne shekarar 2017, inda tun a wancan lokaci ne aka gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo watau Kotu, inda aka yi ta bugawa har sai a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba da aka kammala shari’ar.

Daga karshe dai kotun dake sauraron karar, babbar kotun Musulunci ta jahar Zamfara dake zamanta a garin Gusau ta yanke ma mutanen biyu hukuncin kisa ta hanyar jefewa sakamakon ta tabbatar mutanen sun aikata laifin.

Kamar yadda majiyarmu ya tabbatar, a yanzu ana jiran gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari ne ya rattafa hannu kan hukuncin kisan da aka zartar ma Mainasara da abokinsa domin a cika hukuncin Allah akansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel