Hon. Ibrahim Hasan Buba bai kammala Makaranta ba – UNIJOS

Hon. Ibrahim Hasan Buba bai kammala Makaranta ba – UNIJOS

- Babban Jami’in Jami’ar Jos ya tabbatar da cewa wani ‘Dan Majalisa na rike da takardun bogi

- Jami’ar Tarayyar ta Jos ta bayyana cewa ‘Dan Majalisar bai iya kammala karatu a Jami’ar ba

- Sai dai wani babban Lauya yana kare ‘Dan Majalisar dokokin na Jihar Filato a gaban shari’a

Hon. Ibrahim Hasan Buba bai kammala Makaranta ba – UNIJOS

Jami'ar UNIJOS ta na zargin Ibrahim Buba da amfani da takardun bogi
Source: UGC

Wani babban Jami’in Jami’ar Tarayya da ke Garin Jos watau Monday Danjem ya bayyanawa Kotu cewa ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Filato, Ibrahim Baba Hassan yana amfani ne da takardun jabu domin bai iya kammala Jami’ar ba.

Monday Danjem ya bada shaidar wannan ne a farkon makon nan a gaban wani babban Kotun Tarayya da ke Jos. Danjem yace ‘Dan Majalisar ya gabatarwa Hukumar zabe na INC takardun bogi ne a lokacin da yayi takara a 2015.

KU KARANTA: Gwamnan Filato zai dauki ma'aikata aiki kwanan nan

Jami’ar ta Tarayya da ke Filato tace ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Jos ta Arewa, Ibrahim Baba Hassan, bai kammala karatun Difloman da ya soma ba a shekarun baya inda ya tsere daga Makarantar bayan ya fadi wasu kwas har 6.

Babban Lauya, Solomon Umoh (SAN) wanda yake kare ‘Dan Majalisar yace shaidar da Danjem na Makarantar ya bada da fatar baki, bai isa ba har sai an duba jerin sunayen ‘Daliban da Makarantar tayi tsakanin 1996 har zuwa 2022.

Wannan ‘Dan Majalisar dokokin na Filato da ke wakiltar bangaren Jos ta Arewa yana ikirarin cewa yayi karatun Difloma ne a bangaren harkar kasuwanci a babbar Jami’ar shekaru kadan da su ka wuce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel