Matasa 2 sun yanke kan dan shekara 10 a Lagas

Matasa 2 sun yanke kan dan shekara 10 a Lagas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ama wasu matasa biyu dauke da sabon gawar wani karamin yaro da suka yanke kansa a kan babban titin Ajah zuwa Epe da ke jihar.

Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, CSP Chike Oti ne ya sanar hakan a a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba, inda ya ce jami’ansu masu yaki da garkuwa da mutane ne suka cafke matasan a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 8:30 na dare.

Ya kara da cewa jami’an su sun yi kacibus da matasan biyu ne a yayin da suke gudanar da faturu a kan titin Ajah zuwa Epe, a layin Tunde Balogun da ke a unguwar Shapati, yankin Ibeju-Lekki, jihar Legas.

Matasan, wadanda ‘yan uwan juna ne da suka bayyana shekarunsu da 19 da 18, sun fadawa ‘yan sanda cewa wani ne me suna Sodiq Abefe ya basu kwangilar kawo kan mutum akan kudi N200,000.

Matasa 2 sun yanke kan dan shekara 10 a Lagas
Matasa 2 sun yanke kan dan shekara 10 a Lagas
Asali: Depositphotos

“Mun yaudari yaron ne ta hanyar aikensa ya sayo mana Coca-Cola, ko da ya dawo, sai muka shake shi muka yanke kansa da wuka,” inji wadanda suka aikata laifin.

Iyayen yaron da aka yankewa kan su shaida dansu mai suna Joseph Makinde mai shekaru 10 da haihuwa.

Zuwa yanzu dai ‘yan sanda sun bazama neman Sodiq Abefe, wanda shi ne ya bada kwangilar a samo masa kan mutum.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar taro a kasar Chadi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Imohimin Edgal ya mika lamarin ga sashen bincike akan kisan kai da manyan laifuka don ci gaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel