Boko Haram yanzu na dauko sojin haya daga mayakan kasashen waje - Tukur Buratai

Boko Haram yanzu na dauko sojin haya daga mayakan kasashen waje - Tukur Buratai

- Rundunar sojin Nigeria ta ce yawan hare haren da mayakan Boko Haram ke yi baya rasa nasaba samun agaji ne daga mayakan kasashen waje

- Haka zalika, rundunar sojin ta tabbatar da cewa Boko Haram yanzu na amfani da jirgi maras matuki wajen kai hare hare a sansanonin soji

- TY Buratai ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa a madadin rundunar sojin Nigeria ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a kokarin da suke yi na kare kasarsu ta gado

A ranar Alhamis, rundunar sojin Nigeria ta ce yawan hare hare da kuma kara karfi da mayakan Boko Haram ke yi baya rasa nasaba da cewar 'yan ta'addan na samun agaji ne daga mayakan kasashen waje don taya su kaddamar da hare hare, sakamakon karya lagonsu da aka yi.

Haka zalika, rundunar sojin ta tabbatar da cewa 'yan ta'addan Boko Haram a yanzu na amfani da jirgi maras matuki wajen kai hare hare a sansanonin soji, musamman ma a tsakanin watanni biyu da suka shude.

Birgediya Janar Sani Usman, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a madadin hafsan rundunar sojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai biyo bayan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wani babban sansani yaki na soji da a Maiduguri.

KARANTA WANNAN: A shirye nake mu fafata a taron muhawarar shugaban kasa - Atiku ya shaidawa Buhari

Boko Haram yanzu na dauko sojin haya daga mayakan kasashen waje - Tukur Buratai
Boko Haram yanzu na dauko sojin haya daga mayakan kasashen waje - Tukur Buratai
Asali: Twitter

Ya ce a cikin watanni ukkun, dakarun sojin Nigeria sun kasance suna fuskantar jerin gwanon hare hare ba kakkautawa daga wajen mayakan Boko Haram, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji 39, yayin da 43 suka jikkata a kokarin da jami'an suke yi na kare kasarsu ta gado.

A cewarsa: "A cikin 'yan makwannin nan, dakarun sojin da aka tura shiyyar Arewa maso Gabas karkashin atisayen Lafiya Dole, sun fuskanci hare hare ba adadi daga mayakan Boko Haram. Musamman dakarun sojin da aka tura garuruwan KUKAWA, NGOSHE, KARETO da GAJIRAM wadanda suka fi fuskantar hare hare a cikin makwanni biyu daga ranar 2 zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2018.

"An samu nasarar kwantar da tarzomar dukkanin wadannan hare haren, inda har aka kashe mayakan Boko Haram da dama. Sai dai duk da hakan, an kashe sojoji 16, yayinda aka raunata 12 daga cikinsu kuma suke samun kulawar likita a asibitocin sojoji.

"Kamar yadda kuka sani, Nigeria tura dakarunta zuwa wajen hukumar hadin guiwar jami'an tsaro na kasa da kasa MNJTF da ke da shalkwata a N'djamena, a jamhuriyar Chadi. An kaiwa wata bataliyar dakarun sojin Nigeria na 157 TF Bn da aka tura karkashin MNJTF, hari a wajen wani kauye mai suna METELE a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2018.

"A yayin harin, yanayi ya tilasta dakarun kokarin ja-baya, wanda yayi sanadin mutuwar sojoji 23, yayin da 31 suka jikkata, kuma an kwashe su zuwa asibitin da ke jihar Borno don samun kulawar likita."

TY Buratai ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa a madadin rundunar sojin Nigeria ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a kokarin da suke yi na kare kasarsu ta gado daga harin 'yan ta'adda. Inda ya tabbatar da cewa sadaukarwarsu ba zata tafi a banza ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel