2019: 'Yan Najeriya na ci gaba da marmarin kaɗawa Atiku 'Kuri'un su - PDP

2019: 'Yan Najeriya na ci gaba da marmarin kaɗawa Atiku 'Kuri'un su - PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, 'yan Najeriya sun dukufa akan marmarin kaɗa kuri'un su ga dan takararta na kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar domin kasancewar sa shugaban kasar Najeriya na gaba.

Kakakin jam'iyyar na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin ganawa da shugabannin kungiyar Matasa magoya bayan Atiku daga jihohin Kano, Katsina da kuma Kaduna a babban ofishin jam'iyyar da ke garin Abuja.

Ologbondiyan ya bayyana cewa, 'yan Najeriya na marmarin kada kuri'unsu ga Atiku sakamakon yadda ya haskaka fahimtarsa ta shugabanci a matsayin wata siga ta sadaukar da kai domin inganta jin dadi na wadanda yake jagoranta.

Ya ke cewa, Atiku ya samu karbuwa a zukatan al'ummar kasar nan da ko shakka ba bu zai inganta dukufa tare da sadaukar da kai wajen kyautatawa gami da inganta jin dadi na halin rayuwa na 'yan Najeriya.

2019: 'Yan Najeriya na ci gaba da marmarin kaɗawa Atiku 'Kuri'un su - PDP
2019: 'Yan Najeriya na ci gaba da marmarin kaɗawa Atiku 'Kuri'un su - PDP
Asali: Facebook

Kamar yadda shafin jaridar Leadership ya ruwaito, Ologbondiyan ya bayyana cewa mashahurancin Atiku a fadin kasar nan na ci gaba da yaduwa kasancewarsa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da ya ke ci gaba da razani gami da firgita jam'iyyar APC da kuma dan takararta na kujerar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Sake Zaben Buhari zai inganta Dimokuradiyya a Gwamnatin Najeriya - Jigon APC

Ologbondiyan ya misalta Atiku a matsayin gogaggen dan kasuwa kuma ginshiki mai nasaba da kuma sanadin arziki ta hanyar kawo tsare-tsaren samar da ayyukan yi musamman a tsakankanin Matasa gami da kyawawan manufofi na tunkarar matsalolin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku ya bayyana cewa shugaba Buhari ya kuka da kansa inda zai bambance masa tsakanin aya da tsakuwa yayin taron muhawara na 'yan takarar kujerar shugaban kasa da za a gudanar a watan Jibi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel