Badakalar kudi: An gurfanar da Farfesa Fatima ta makarantar Dadin-Kowa

Badakalar kudi: An gurfanar da Farfesa Fatima ta makarantar Dadin-Kowa

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da Farfesa Fatima Sawa, shugabar makarantar koyon aikin lambu da ke garin Dadin-Kowa a jihar Gombe.

EFCC ta gurfanar da Farfesa Fatima ne tare da Abdurrashid Abubakar da Umar Modibbo na ofishin hada-hadar kudade na makarantar bisa zarginsu da almundahanar kudi da yawansu ya kai miliyan N52.4m.

EFCC na zargin mutanen uku da yin amfani da matsayinsu na kasancewar shugabanni a makarantar wajen karkatar da kudaden daga asusun makarantar zuwa asusun wani kamfani, "Freeman ICT Hub", da binciken EFCC ya gano cewar babu kwangilar aiki kowacce iri tsakaninsa da makarantar.

Badakalar kudi: An gurfanar da Farfesa Fatima ta makarantar Dadin-Kowa
Badakalar kudi: An gurfanar da Farfesa Fatima ta makarantar Dadin-Kowa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar dokokin jihar APC sun tafi yajin aiki saboda rashin biyansu alawus

Lauyan hukumar EFCC, Ndeh Godspower, ya shaidawa kotu cewar Farfesa Fatima da ragowar mutanen biyu sun karkatar da kudaden zuwa asusun kamfanin a rana daya.

Sai dai, dukkan mutanen sun ki amincewa da tuhuma 4 da ake yi ma su.

Wannnan cijewa da su ka yi ne ya sa lauyan hukumar EFCC ya nemi kotu ta tsare wadanda ake zargin zuwa sabuwar ranar da zata tsayar domin cigaba da sauraron karar.

Sai dai alkalin kotun, Jastis Nehizena Idemudia, ya amince da bayar da belin mutanen uku kamar yadda lauyansu ya roka tare da saka ranar 17 ga watan Janairu domin cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel