Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya ziyarci dakarun sojojin da aka raunata

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya ziyarci dakarun sojojin da aka raunata

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau Laraba, 28 ga watan Nuwamba ya ziyarci dakarun sojojin Najeriya da yan ta’addan Boko Haram suka ji wa rauni a harin Matele.

Shugaban kasar ya jinjina masu tare da yaba ma namijin kokarin da suke yi don ganin sun kare kasar da al’umman kasar daga duk wani hari.

Ya kuma yiwa sojojin da suka rasu a filin daga addu’an Allah ya ji kansu.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya ziyarci dakarun sojojin da aka raunata
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya ziyarci dakarun sojojin da aka raunata
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: An cire Buhari da Atiku daga tattaunawar shugabannin Kiristoci

“A yau na ziyarci dakarun sojin da suka samu rauni. A fadin arewa maso gabas muna da jaruman sojoji da ke aiki ba tare ba rana don ganin sun tsare kasar mu daga ta’addanci da rikici. Ina jinjinawa sadaukarsu a madadinmu. Kuma Allah ya ji kan wadanda suka rasu,” kamar yadda Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A baya mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da dogon jawabi a birnin Maiduguri, jihar Borno a yau Laraba yayinda ya tafi halartan taron babban hafsan sojin Najeriya da ke gudana a jihar.

Buhari ya yi Allah wadai da yadda wasu yan siyasa ke amfani da rashin da sojojin sukayi sakamakon harin da yan Boko Haram suka kai kwanakin nan inda ya zaburar da Sojin da su cigaba da jajircewa duk da makircin makirai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel