Tsananin matsin rayuwa ta kai wani ma’aikacin gwamnati ga rataye kansa da kansa har lahira

Tsananin matsin rayuwa ta kai wani ma’aikacin gwamnati ga rataye kansa da kansa har lahira

Wani mutumi mai shekaru 49, Abolarin Olaoye dake aiki da hukumar bada tallafin karatu ta jahar Ekiti ya kashe kansa, inda aka wayi gari aka tsinci gawarsa tana reto a saman iska bayan rataye kansa a babbar sakatariyar ma’aikatan jahar Ekiti.

Majiyar Legit.com ta bayyana cewa Abolarin ya fito ne daga kauyen Igogo Ekiti ta cikin karamar hukumar Moba, kuma yayansa biya, amma ya kashe kansa ne saboda tananin wahalar rayuwa daya tsinci kansa a ciki da kuma dimbin bashin daya taru akansa.

KU KARANTA: Wani dan tatsitsin yaro mai shekaru 16 ya halaka budurwarsa saboda tana neman Yayansa

An hangi jama’a da dama da suka hada da abokan aikinsa da ma wasu ma’aikata da suka fito daga sauran ofisoshin dake sakatariyar suna taru gungu gungu a hawa na daya inda gawar take reto suna tattauna lamarin mutuwar Abolarin, lamarin da suka ce ya daure musu kai.

Baya ga aikin da mamacin keyi da hukumar bada tallafin karatu ta jahar Ekiti, haka zalika yana aikin achaba idan ya tashi aiki kuma yana taba noma, amma fa duk da haka yana kokawa da tsananin wahalan rayuwa, inda ya danganta hakan ga rashin samun albashi akai akai.

Ba tare da bata lokaci ba ne jami’an Yansanda da na hukumar tsaron farin kaya, DSS, suka hallara a ma’aikatan, sai dai basu sauko da gawar ba har sai da suka jira iyalai da yan uwan mamacin suka iso suka ga gawan da kansu yadda ya kashe kansa.

Wata surukarsa, Elizabeth Babalola ta bayyana ma majiyarmu cewa Abolarin ya kai mata ziyara a ranar Talata da misalin karfe 4;30 na rana, inda yayi mata korafin mawuyacin halin da yake ciki. “Da misalin karfe 4:30 na ranar Talata ya zogidana.

“Yayi min korafin halin da yake ciki, musamman cewa hayansa ya kare, kuma bashi da halin sake biyan wani kudin hayan saboda albashinsa baya zuwa akai akai, wata matsalar kuma shine ya karbi bashin kudin sayan gida dana sayan mota daga gwamnati, amma duk bai saya ba, don haka ana cirewa a albashinsa

“Ga matsalar iyali da yace ya dameshi, saboda baya iya taimaka ma dangin matarsa, don haka ya fada min karara cewa shifa zai iya aikata ma kansa sabalikita, domin a cewarsa ya gaji da rayuwar, gaskiya ban dauka zai iya kai ga haka ba.” Inji ta.

Shima shugaban hukumar bada tallafin karatu, inda mamacin ke aiki, Ayo Ajimat ya tabbatar da mutuwar Abolarin, sai dai yace sun yi mamakin wannan mataki daya daukan ma kansa, saboda mutum ne mai faran faran da mutane, inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel