Zan yi murabus idan APC ta lashe zaben jiha ta - Babban Sarki a arewa

Zan yi murabus idan APC ta lashe zaben jiha ta - Babban Sarki a arewa

Sarkin Ilorin, Alhaji Dakta Ibrahim Sulu Gambari, ya bayyana goyon bayansa ga takarar Barista Razak Atunwa, dan takarar gwamnan jihar Kwara a inuwar jam'iyyar PDP, kamar yadda masarautar Ilorin ta sanar yayin hudubar sallar juma'a a babban masallacin garin Ilorin.

Sarkin ya nuna rashin jin dadinsa bisa yadda jam'iyyar APC ta yiwa shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, butulci duk da irin wahalar da ya yi ma ta kafin zaben shekarar 2015.

Sarkin ya bayyana cewar rashin bin Saraki a hankali ne ya jawowa Buhari shan wahalar tafi da mulkin Najeriya tare da kari da cewar rashin kokarin Buhari a mulki na da alaka da wofantar da Saraki da ya yi.

Zan yi murabus idan APC ta lashe zaben jiha ta - Babban Sarki a arewa
Sarkin Ilorin, Alhaji Dakta Ibrahim Sulu Gambari
Asali: Facebook

"Ko yanzu da mu ke magana Kwara na da ruwa mai tsafta domin amfanin yau da kullum, hakan na daga cikin kokari da bin tsarin da Saraki ya dora jihar a kai kuma gwamna Abdulfatai Ahmed ke bi," a cewar Gambari.

Sarkin ya koka a kan yadda binciken kwangilar hanyar Jebba a gwamnatin Buhari ya so tozarta shi ba don Saraki ya cece shi ba.

DUBA WANNAN: Yunkurin tsigewa: Buhari zai san makomansa a watan Disamba

"Na yarda da dan mu, duk inda Saraki ya shiga muna tare da shi," a cewar Sarki Gambari. Sannan ya kara da cewar idan shugaba Buhari ya samu ko da kashi 30% na kuri'un jihar Kwara a zaben 2019, zai sauka daga kujerar sa tare da yin hijira tare da fadin cewar ya san jama'ar jihar Kwara ba zasu sake zaben Buhari ba ko don su kare mutuncin gidan sarautar jihar.

Wannnan ba shine karo na farko da Sarkin na Ilorin ya fito bainar jama'a ya nuna goyon bayansa ga Saraki ko sukar Buhari ba. Ma su bibiyar siyasar jihar Kwara sun ce biyayyar da Sarkin ke yi ga Saraki ne ta sa ake bashi manyan kwangiloli a jihar Kwara.

Sai dai wasu jama'ar masarautar Ilorin sun bayyana kalaman Sarki Gambari a matsayin holoko da harbin iska. Yanzu abin jira shine a zuba ido don ganin ko Sarkin zai iya cika wannan barazana da ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel