Bacci ya sace direban jirgin sama yana tuki

Bacci ya sace direban jirgin sama yana tuki

Hukumomin da ke kula da lafiyar jiragen sama sun ce wani karamin jirgi da ya kamata ya sauka a Australia ya wuce inda ya kamata ya sauka da kimanin kilomita 50 saboda bacci ya kwashe direban jirgin.

Direban jirgin ne kadai ke cikin jirgin mai kirar Piper PA-31 a yayinda ta taso daga Devonport zuwa King Island da ke Tasmania a ranar 8 ga watan Nuwamba kamar yadda BBC ta ruwaito.

Bacci ya sace direban jirgin sama yana tuki
Bacci ya sace direban jirgin sama yana tuki
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamna Yari ya dakatar da sarakuna hudu a Zamfara

Hukumar da ke kula da harkokin jiragen sama ta Australia ATSB na gudanar da bincike a kan afkuwar lamarin.

Kawo yanzu, hukumomin ba su bayyana yada direban jirgin ya farka kuma ya sauka daga jirgin ba tare da wata matsala duk da cewa ya wuce ainihin inda ya kamata ya sauka.

Hukumar ta ATSB ta ce za ta yiwa direban jirgin tambayoyi kuma za tayi bincike kan yadda kamfanin ke gudanar da harkokinta kafin ta fitar da rahoto a 2019.

A bara, mutane biyar sun rasa rayyukansu yayin da wani jirgi da zai tafi King Island ya yi hatsari bayan ya taso daga Melbourne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164